Kiwon Lafiya
Ministan sufuri ya ce bai ji dadin yarda aikin gina layin dogo da ya tashi zuwa Lagos ke tafiya ba
Ministan sufuri Rotimi Amaech yace bai ji dadin yadda dan kwangilar dake aikin gina layin dogo da ya tashi daga Lagos zuwa badin yake gudanar da aikin sa ba.
Rotomi Amaechi yayi mamakin yadda aikin yake tafiyar hawainiy a lokacin da yake ziyarar aiki na wata-wata a jiya kan manyan ayyukan da gwamnatin tarayya ta kaddamar a jiya Talata a birnin Badin.
A rahoton da dan kwangilar ya bayar ana zaton cewa zai sauya wa wasu bututun ruwa waje da ya shafi aikin layin dogo, amma kuma ya gazza yin hakan.
A cewar Rotomi Amaechi kamata yayi dan kwangilar ya fara aikin sauyawa bututun da wuri, kamar yadda ya alkawarta amma sai ya gaza yin hakan, bayan da ya ce zai kamamla aikin kafin nan da ranar 2 ga watan Nuwanba mai kamawa, sai dai yawan kawo uziri na rashin aikata hakan
Haka zalika ministan na sufuri ya ce alhakin dan kwangilar ne ya gina tashohin jiragin kasa guda 10 da zai tashi daga Lagos zuwa badin, wanda zai baiwa al’ummar yankin damar yin amfani da tashohin jiragin kasa wajen gudanar da al’amuran yau da kullum.