Labarai
Gwamnati ta musanta zargin hannu a yunkurin juyin mulkin Nijar

Gwamnatin tarayya ta musanta zargin cewa ita ko ƙungiyar Ecowas sun goyi bayan wani yunƙurin juyin mulki da ake zargin an yi a Jamhuriyyar Nijar.
Ma’aikatar Harkokin wajen kasar nan ta ce zarge-zargen da ake yaɗawa a kafafen sada zumunta ba su da tushe, kuma yunƙuri ne na yaudarar jama’a da ɓata sunan ƙasar.
Wani jami’in sojin Nijar, Kyaftin Roger Gabriel, ya zargi wasu ƙasashen waje da kuma mutanen da ke da alaƙa da tsohon shugaban ƙasar, Mohamed Bazoum, da ƙoƙarin tsoma baki a rikicin da ya faru a wani sansanin soji da ke Niamey.
Gwamnatin ta ce ba za ta goyi bayan duk wani sauyin gwamnati da ba bisa tsarin mulki ba, tana mai jaddada goyon bayanta ga matsayar Ecowas da Tarayyar Afirka kan kin amincewa da juyin mulki.
Dangantakar Najeriya da Nijar ta yi tsami tun bayan juyin mulkin da sojoji suka yi a Nijar a watan Yulin 2023, wanda ya hambarar da gwamnatin Mohamed Bazoum.
You must be logged in to post a comment Login