Addini
Muhimman abubuwan da ya kamata ku sa ni kan Sheikh Ja’afar Mahmud
An haifi Sheikh Ja’afar Mahmoud Adam a garin Daura, a shekara ta 1962 ko da yake wani lokacin Yakan ce 1964.
Marigayi Sheikh Ja’afar ya fara karatunsa na allo a gidansu, a hannun Mijin Yayarsa, Mallam Haruna, wanda kuma dan uwansu ne na jini.
Daga nan kuma sai aka mayar da shi wajen Malam Umaru a wani gari Koza, Kimanin kilomita 9 a arewa da Daura, wanda shi ma akwai
dangantaka ta jini.
Bayan sun zo Kano ne tare da wannan malami nasa, a shekara ta 1971 (ko 1972), sai suka zauna a makarantar Malam Abdullahi, wanda asalin sa mutumin jamhuriyar Nijar ne, amma yake zaune a unguwar Fagge a Kano.
Kafin zuwan sa Kano, marigayi Sheikh Ja’afar ya riga ya fara haddar Alkur’ani mai girma, wanda ya kammala a shekara ta 1978.
Bayan da Malam ya kammala haddar Alkur’ani mai girma, kasancewar sa mai sha’awar ilimi, sai ya shiga makarantu biyu a lokaci daya a shekara ta 1980, ya shiga makarantar koyon Larabci ta mutanen kasar Misra a cibiyar yada Al ‘ Adun Misra.
Sheikh jafar ya kuma shiga makarantar Larabci ta Gwale a shekara ta 1984, kuma ya kammala a shekara ta 1988.
A shekara ta 1989, ya sami gurbin karatu a jami’ar musulunci ta Madinah, a inda ya karanta Ilimin Tafsiri wanda kuma ya kammala a Shekara ta 1993.
Sheikh Ja’afar ya sami damar Kammala karatun digiri na biyu Masters a Jami’ar Kasa-Da-Kasa Ta Afrika da Take Khartoum a, Sudan daga nan ne kuma sheikh jafar ya fara aikin yada addinin musulunci da karantar da mutane musamman a masallacin sa na Almuntada dake unguwar Dorayi, wanda kuma anan ne wasu ‘yan bidiga suka harbe shi, a ranar 13 ga watan Afrilun shekarar 2007 lokacin da ya ke limancin sallar Asuba wanda hakan yayi sanadiyyar rasuwar sa.
Daga cikin karatuttukan da Sheikh Ja’afar ya karantar da su, sun hada da tafsirin Alkur’ani mai Girma, kitabuttauhiid, Umdatul Ahkaam, Arba’un Hadith, Kashfusshubuhaat, Bulugul Maraam, Riyaadussalihiin, Siiratun Nabawiy, Ahkaamul Janaa’iz, Siffatus saltin nabiiy.
Da fatan Allah ya yi masa rahmah !
You must be logged in to post a comment Login