Connect with us

Labarai

Mun ceto yara fiye da 180 da aka yi safararsu- NAPTIP

Published

on

Hukumar hana fataucin mutane ta Najeriya NAPTIP, ta ce, ta ceto yara sama da 180 da aka yi safararsu daga jihohin Kaduna, Anambra, Benue, Nasarawa da wasu wurare.

 

Hukumar ta bayyana cewa wasu ƙungiyoyin masu fataucin yara na yaudarar iyaye ta hanyar bayyana kansu a matsayin ma’aikatan ƙungiyoyin farar hula masu tallafa wa yara da ilimi, sannan su tafi da yaran da sunan ba su ilimi da tallafi.

 

A baya-bayan nan, an ceto wasu yara uku da aka kwaso daga Kajuru a jihar Kaduna a wani gini da ke Onitsha ta jihar Anambra, yayin da aka kuma gano wani yaro a hannun wata ma’aikaciyar lafiya.

 

NAPTIP ta ce wasu daga cikin yaran da aka ceto an kai su gidajen marayu inda aka rika sayar da su ga mutane da sunan ɗaukar yara reno.

 

Hukumar ta ce tana ci gaba da farautar masu hannu a wannan laifi domin gurfanar da su a gaban kuliya.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!