Labarai
Gwamna Abba ya bukaci Musulmi su yi amfani da Takutaha wajen koyi da kyawawan halayen Ma’aiki

Gwamnan jihar Kano Alhaji Kabir Yusif ya bukaci al’ummar musulmi da su yi amfani da ranar Takutaha wajen yin koyi da kyawawan halayen Annabi Muhammad Sallallahu-alaihi wasallam.
Hakan na cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa Alhaji Sunusi Bature Dawakin Tofa ya fitar.
Sanarwar ta kuma ce, zaman Lafiya da Garkiya da Tsoran Allah da kyautatawa na daga cikin halayen annabi da ya kamata kowanne Musulmi yai koyi da su.
A cewar sanarwar duba da muhimmancin ranar ne yasa gwamnatin jihar Kano ta bayar da hutu domin gudanar da murnar haihuwar Annabin tsira Annabi Muhammad Sallallahu Alaihi Wasallam.
You must be logged in to post a comment Login