Manyan Labarai
Mun kama masu fataucin bil Adama fiye da 116 – NAPTIP
Hukumar yaki da fataucin bil Adama ta kasa NAPTIP ta ce, ta kama masu fataucin bil Adama dari da goma sha shida ya yin da kuma ta ceto mutane dubu daya da dari hudu da tamanin da tara cikin shekaru 4.
Kwamandan shiyyar Kano Shehu Umar ne ya sanar da hakan a tattaunawar sa da manema labarai a nan Kano.
Shehu Umar ya kara da cewar, hukumar ta karbi rahoton yin fataucin bil Adama dubu daya da dari biyar da goma sha shida wanda ya hadar da mutane dubu daya da goma sha hudu a ciki da wajen jihar nan.
Kwamadan ya kara da cewar, hukumar ta kuma kama mutane 91 maza da mata 25 da ake zargin suna safarar bil Adama.
Yana mai cewar daga cikin rahoton akwai 117 na cin zarafin kanana yara da 75 masu bautar da kananan yara da kuma masu cin zarafin mata wanda hukumar ke yaki da shi da ya yi dai-dai da dokar da ta kafa ta NAPTIP na shekara ta 2016 kawo watan Yulin wannan shekarar.
You must be logged in to post a comment Login