Labarai
Mun kammala gyara matsalolin da muka fuskanta a zaben shugaban kasa- INEC
Hukumar INEC ta ce, ta gyara dukkan matsalolin da ta fuskanta a yayin zaben shugaban Kasa da na yan majalisun tarayya, gabanin zaben gwamnoni da za a gudanar a karshen makon nan.
Kwamishinan hukumar mai kula da wayar da kan masu zabe Festus Okoye, ne ya bayyana hakan yayin tattaunawarsa da manema labarai.
Ya ce INEC ta koyi muhimman darussa, kuma za ta yi amfani da su wajen gyara matsalolin da za a iya fuskanta a zaben na gwamnoni.
Festus Okoye, ya kuma ce, sun yi iya bakin kokarinsu wajen tabbatar da an magance matsalar sashen duba sakamakon zabe na shafin hukumar.
Ya kara da cewa, yanzu haka sashen yada labara na hukumar ya yi shirin ko ta kwana, ko da za a fuskanci kalubale yayin dora sakamakon zabe daga rumfunan zabe a shafin hukumar.
Ko a makon da ya gabata, sai da kotun daukaka kara ta amince wa hukumar INEC da ta sake sabunta bayanan da ke kan na’urar tantance masu zabe ta BVAS gabanin zaben na karshen mako.
Sai dai daga bisani INEC ta sanar da dage zaben zuwa ranar 18 ga watan Maris, maimakon 11 ga wata domin samun damar sabunta bayanan.
You must be logged in to post a comment Login