Labarai
Mun shawo kan ɓarkewar Kwalara a ƙananan hukumomi 14- Gwamnatin Zamfara

Gwamnatin jihar Zamfara ta ce ta yi nasarar shawo kan ɓarkewar cutar kwalara da ta addabi al’ummomi da dama a ƙananan hukumomi 14 na jihar.
Wata sanarwa daga ma’aikatar lafiyar jihar ta ce kwamishiniyar lafiya, Dakta Nafisa Maradun ce, ta bayyana hakan yayin taron duba matakan da aka ɗauka wajen yaƙi da kwalara, da aka gudanar a cibiyar ayyukan gaggawa ta kiwon Lafiya a Gusau.
Dakta Nafisa ta bayyana cewa an samu adadin mutum 15,464 da suka kamu da kwalara, inda aka yi wa 15,265 magani kuma aka sallame su, yayin da mutum 192 suka rasa rayukansu a kananan hukumomi 14 na jihar.
Kwamishiniyar ta ce gwamnatin jihar ta samar da ingantaccen tsarin shirin kariya daga Annoba domin magance duk wani barazana ga lafiyar jama’a nan gaba.
You must be logged in to post a comment Login