Manyan Labarai
Muna goyon bayan ilimi kyauta kuma wajibi -sabon Sarkin Kano
Sabon sarkin kano Alhaji Aminu Ado Bayero, ya jaddada goyon bayan sa ga shirin ilimi kyauta kuma wajibi na gwamnatin jihar Kano.
Mai martaba Aminu Ado Bayero, yace zasu yi duk mai yiwuwa karkashin ikon su don ganin shirin ya tabbata da amfanar da al’umma, san nan ya yi kira ga dukkanin Al’umma dasu mayar da hankali wajen taimakawa makarantu a wani mataki na bunkasa harkokin ilimi a fadin jihar nan.
Sabon sarkin, ya bayyana hakan ne a yayin ziyarar da ya kai makarantan firamare ta gidan makama don duba halin da karatun makarantar yake gudana.
Sabon Sarkin Kano yaje gidan mahaifiyar sa don neman tabarraki
Ana tsaka da nada sabon sarkin Bichi
Mai martaba Aminu Ado Bayero, ya ce wajibi masu hannu da shuni da su shigo cikin harkokin sha’anin ilimi domin kuwa gwamnati kadai baza ta iya ba.
A nasa jawabin shugaban hukumar kula da makarantun sakandire na jihar kano, Dr Bello Shehu, ya nemi hadin kan masarautun gargajiya don ganin shirin ya cimma nasara.
Shamsu Dau Abdullahi, wakilin mu da ya halarci wajen taron ya ruwaito cewar yayin ziyarar sabon sarkin ya samu rakiyar manyan hakiman sa.
You must be logged in to post a comment Login