Connect with us

Labarai

Mutane 19 sun rasu sakamakon sabon rikicin Rasha da Ukraine

Published

on

Rikicin da ke tsakanin Rasha da Ukraine na baya-bayan nan ya yi sanadin mutuwar akalla mutane 19, yayin da kasashen biyu ke ci gaba da kai hare-haren jiragen sama marasa matuka da makamai masu linzami kan wurare daban-daban.

 

A Rasha, mutane biyar sun mutu a wani hari da jiragen Ukraine marasa matuka suka kai a yankin Rostov, yayin da wasu mutane uku suka mutu a wasu yankuna. Ma’aikatar tsaron Rasha ta ce ta kakkabo jirage marasa matuka 822 cikin dare.

 

A Ukraine kuma, hare-haren Rasha sun kashe mutane a yankunan Kryvyi Rih, Zaporizhzhia, Sumy da Donetsk, yayin da aka lalata wasu cibiyoyin masana’antu da kasuwanni. Shugaban Ukraine, Volodymyr Zelensky, ya ce hare-haren sun kara muni, yana kuma neman kasashen kawance su kara samar wa Ukraine da makaman kare sararin samaniya.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!