Labarai
Mun fara bin diddigin wasu daga cikin manyan masu safarar kwayoyi- Barr. Muhyi

Kwamitin yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi na jihar Kano ya ce ya fara bin diddigin wasu daga cikin manyan masu safarar miyagun kwayoyi a jihar.
Shugaban kwamitin, Muhyi Magaji Rimin Gado, ya bayyana hakan ne yayin tattaunawarsa da wakilinmu Nura Bello.
Ya ce, kwamitin ya fara kai mutanen da ya ke kama wa zuwa cibiyar gyaran hali da dabi’a da ke karamar hukumar Kiru, domin ba su damar samun kulawar da ta dace.
You must be logged in to post a comment Login