Labarai
Mutane 5 sun rasu sakamakon rushewar gine-gine biyu a Kano

Mutane biyar sun mutu, yayin da wasu 10 suka tsira da ransu bayan rugujewar wasu gine-gine guda biyu a jihar Kano ranar Asabar.
Hukumar kashe gobara ta jihar Kano ta ce ginin da ake ginawa a unguwar Gaida, karamar hukumar Kumbotso, ya ruguje kan ma’aikata shida. Biyu daga cikinsu sun tsira da ransu, yayin da wasu hudu suka mutu bayan ceto su cikin sume.
A wani lamari na daban a Kurna, karamar hukumar Fagge, ginin makarantar Islamiyya mai suna Khadija Idris Bala ya rufta kan dalibai tara.
Ta cikin wani sakon murya da ya aikewa manema labarai, mai magana da yawun hukumar ACFO Saminu Yusuf Abdullahi ya ce, takwas daga cikinsu sun tsira, yayin da daliba daya mai suna Khadija Muhammad, mai kimanin shekara 14, ta mutu.
Hukumar kashe gobarar ta ce har yanzu ana bincike domin gano musabbabin rugujewar gine-ginen, tare da gargadin masu gine-gine da ‘yan kwangila su kiyaye ka’idojin tsaro, musamman a lokacin damina
You must be logged in to post a comment Login