Labarai
Mutane 21 sun mutu a gobarar da ta tashi a Delhi

Aƙalla mutum 21 sun mutu, yayin da wasu da dama suka jikkata bayan da gobara ta tashi a wani babban gini mai tsawo a Delhi.
Marasa lafiya da ƴan uwansu da ke karɓar kulawa a wani asibiti mai zaman kansa da ke kusa ne ke zama a ginin da gobarar ta tashi.
Rahotanni sun bayyana cewa da dama daga cikin wadanda lamarin ya rutsa da su ƴan ƙasashen waje ne, kamar Najeriya, Mozambique da Bangladesh da Laberiya, waɗanda suka je India domin neman lafiya, ko kuma suka rako ƴan uwansu da ba su da lafiya.
Shaidu sun bayyana cewa wutar ta yi ta bazuwa cikin sauri, lamarin da ya sa waɗanda ke sama kasa tserewa.
Wakilin BBC ya ruwaito cewa ƴan sanda sun ce an kashe gobarar, sai dai har zuwa fitar da wani rahoto ba a san musababin tashinta ba.
You must be logged in to post a comment Login