Labarai
Mutane 30 sun rasu a hatsarin mota a hanyar Kano zuwa Zaria
Kimanin mutane talatin ne suka rasu, tare da jikkatar goma sha biyu, a wani hatsarin mota da ya afku a hanyar Kano zuwa Zaria.
Babban jami’in hukumar kiyaye afkuwar haɗura ta ƙasa FRSC shiyyar Zaria, ACC Abdurrahman Yakasai ne ya tabbatar ga hakan ga Freedom Radio.
Ya ce, hatsarin ya afku ne da yammacin ranar, Alhamis a daidai garin Tashar Musa da ke ƙaramar hukumar Maƙarfi ta jihar Kaduna.
Motocin da hatsarin ya rutsa da su sun haɗar da Hummer Bos ƙirar Toyota mai ɗaukar mutane 18, da kuma wata motar Volkswagen saloon a cewarsa.
AAC Abdurrahman Yakasai, ya ce hatsarin ya faru ne sakamakon gudin wuce ƙima da ƙoƙarin wuce na gaba da direbobin ke yi, ba tare da la’akari da sauran matafiya ba.
Sai dai ya ce, basu iya tantance lambobin motocin ba saboda ƙonewar da suka yi, amma suna ci gaba da bincike.
Wakilin Freedom Radio Hassan Ibrahim Zariya ya rawaito cewa, tuni aka garzaya da gawarwakin da waɗanda suka jikkata zuwa asibitin koyarwa na jami’ar Ahmadu Bello.
You must be logged in to post a comment Login