Kiwon Lafiya
Mutane 60 ne suka mutu sanadiyyar cutar Amai da Gudawa a Abuja – FCTA
Gwamnatin Babban Birnin Tarayya Abuja na cigaba da wayar da kan al’umma game da barkewar cutar amai da gudawa da tayi kamari a yanzu.
Ministar Babban Birnin Tarayyar, Dakta Ramatu Aliyu ce ta bayyana haka yayin gangamin wayar da kan al’umma game da cutar a yankin Pyakasa da Gwagwa dake Abuja.
Kawo yanzu, adadin wadanda suka mutu sakamakon cutar ya karu daga 54 zuwa 60.
Haka zalika, wadanda ake zaton sun kamu da cutar a yankin sun tashi daga 604 zuwa 698 cikin kwanaki 3.
Ministar ta bukaci mazauna birnin na FCT da masu ruwa da tsaki da su sanar da hanyoyin da al’umma za su bi wajen yin rigakafin cutar da tsaftace muhalli tare da kiyaye tsabtar hannuwa a koda yaushe.
You must be logged in to post a comment Login