Labarai
Ku haɗa kai wajen kawo ƙarshen matsalar tsaro a Najeriya – Abdulsalami Abubakar

Tsohon Shugaban Ƙasa na mulkin soja, Janar Abdulsalami Abubakar mai ritaya, ya bukaci ‘yan Najeriya da su haɗa kai domin kawo ƙarshen matsalar tsaro da ta addabi ƙasar nan.
Janar Abdulsalami Abubakar ya ce yaƙi da ta’addanci da sauran laifuffuka ba aikin jami’an tsaro kaɗai ba ne, kowa yana da rawar da zai taka.
A cikin saƙon da ya fitar yayin bikin cika shekaru 84 da haihuwarsa, Abdulsalami ya nuna damuwa kan yadda rashin tsaro ke ƙara ta’azzara, inda ya ce mutuwar Manjo Janar Abubakar Rabe da sauran waɗanda suka rasa rayukansu na nuna buƙatar haɗin kai cikin gaggawa.
Ya yi gargadin cewa siyasantar da batutuwan tsaro da kuma yaɗa labaran ƙarya a kafafen sada zumunta na ƙara ba ƙungiyoyin ta’adda ƙarfi.
Saboda haka, ya buƙaci ‘yan Najeriya su ajiye bambance-bambancen ƙabila, addini da siyasa, su haɗa kai da gwamnati da jami’an tsaro domin dawo da zaman lafiya.
You must be logged in to post a comment Login