Manyan Labarai
Na baiwa Freedom Radio Award ne saboda yadda take ilmantar da al’umma
Da tsakar ranar yau Talata 18 ga watan Faburairu ne wani magidanci dan asalin garin Jalingo babban birnin jihar Taraba ya ziyarci tashar Freedom Radio Kano tare da baiwa tashar shaidar girmamawa watau Award.
Magidancin mai suna Malam Nuru Umaru Aliyu ya bayyan cewa ya dade yana bibiyar yadda tashar ta Freedom Radio ke gudanar da shirye-shiryenta duk lokacin da ya zo jihar Kano, har ma ta kai gay ana bibiyar tashar ta shafukanta na Internet har ma da sababbin manhajojin zamani da ake iya sauraron tashar.
Haka kuma ya kara da cewa ya dade yana son ya ziyarci tashar domin ziyarar gani da ido kan yadda take gudanar da ayyukanta tare da bayyana irin soyayyar da yake yiwa tashar, said ai bai samu dama ba sai a yau.
Malam Nuru Umaru Aliyu ya kuma bayyana cewa, shi kadai ya yanke shawarar karrama tashar da shaidar girmamawa kuma ko da ya zo bada shaidar girman sai ya ga tashar ta ma wuce duk yadda yake tunani ta fannin yadda ma’aikatanta ke gudanar da aikinsu.
Ya kuma ce akwai shirye-shiryen da tashar take gudanarwa da yake matukar kaunarsu wadanda suka hadar da Shirin Inda Ranka da Barka da Hantsi da kuma shirin Allah daya Gari Ban-ban da suaransu.
Ko da aka tambaye shi kan ko akwai wani shiri dake bukatar gyara a tashar? Sai ya ce, akwai bukatar a kara inganta shirin Birni da Karka domin shiri ne mai matukar muhimmanci.