Labarai
Na koma aikin gini da sharar kwata – Mamallakin makaranta a Kano
Matsalar rufe makarantu da aka yi ciki har da masu zaman kansu a Kano ya tilastawa wani shugaban makaranta mai zaman kanta shekaru hamsin da biyar a duniya fara neman aikin sharar kwata da aikin gini sakamakon mawuyacin halin da ya tsinci kansa na rashin kudi da aikin yi.
Tun da fari mutumin mai suna Malam Hussain Abdulhamid Muhammad ya shaidawa wakilin gidan Radio Freedom Abdulkarim Muhammad Tukuntawa cewa ya dauki wannan matakin ne sakamakon bashida wata sana’a da yake gudanarwa a yanzu.
Malam Hussain ya kara da cewa yanada iyali ga kuma tarin ‘ya’ya da yake dasu wanda hakan ya tilasta masa daukar wannan mataki domin rufawa kansa asiri dana iyalinsa.
Hussain Abdulhamid ya kuma shawarci gwamnatin jihar Kano da ta kawowa malaman makarantu masu zaman kansu dauki sakamakon mawuyacin halinda suke ciki a yanzu.
Ya kara da cewa rayuwar malaman makarantu masu zaman kansu a yanzu na cikin garari, saboda ci gaba
da rufe makarantu da ake yi sakamakon bullur annobar cutar covid 19.
You must be logged in to post a comment Login