Labarai
Na shirya tsaf domin yakar zazzabin Malaria – Ganduje
A baya-bayan nan ne gwamnatin Kano ta sanar da cewa za ta kaddamar da shirin bayar da tallafi ga mata masu juna biyu da kananan yara, yayinda za a yiwa yaran da basu wuce watanni uku zuwa shekarua biyar na haihuwa ba rigakafin zazzabin cizon sauro.
Yayinda kaddamar da shirin raba magunguna rigakafin cutar ta maleriya a jiya Lahadi a garin Bichi, gwamnatin Kano ta ce za ta kashe naira biliyan uku domin shawo kan matsalar zazzabin cizon sauro a fadin jihar.
Gwamnan Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje wanda ya bayyana hakan a taron kaddamar shirin, y ace yayinda ake samun yawaitar matsalar zazzabin maleriya, musamman a wannan yanayi na damuna ya sanya gwamnati ta tashi tsaye domin tunkarar matsalar.
Gwamnan ya ce abinda suka fi mayar da hankali a kai shine lafiyar mata masu juna biyu da kananan yara, inda ya ja hankalin iyaye su bawa gwamnati hadin kai.
Shima a nasa jawabin, mai martaba sarkin Bichi Alhaji Nasir Ado Bayero ya yi kira ga mutane, musamman wadanda shirin ya shafa da su rungumi tsarin rigakafin hannu biyu, da kuma bin dokokin yaki da annobar Covid-19 da gwamnatin Kano ta gindaya.
Gwamnatin Kano za a dauki tsawon mako guda ana gudanar da shirin rigakafin zazzabin cizon Sauron a kananan hukumomin Kano guda 44.
You must be logged in to post a comment Login