Labarai
NAHCON, ta ce jirgin farko na maniyyatan bana zai tashi ne daga birnin Owerri

Hukumar jin dadin alhazai ta kasa NAHCON, ta ce, jirgin farko na maniyyatan bana zai tashi ne daga birnin owerri na jihar Imo.
Hakan na cikin wata sanarwa da mai magana da yawun hukumar Fatima Usara, ta fitar tana mai cewa maniyyata 315 daga jihohin Imo da Abia da Bayelsa ne za su tashi a jirgin kamfanin Air Peace.
Fatima Usara ta kuma ce, tun a jiya Laraba ne tawagar hukumar ta NAHCON ta isa Owerri domin sanya ido kan shirye-shiryen jigilar maniyatan.
Jami’ar ta ce ana sa ran cewa jirage hudu ne za su tashi a rana guda.
You must be logged in to post a comment Login