Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Coronavirus

Najeriya ta shekara 2 da samun ullar cutar Corona

Published

on

A ranar Lahadi 27ga watan Fabrairun 2022 ne Najeriya ta cika shekara biyu da samun rahoton bullar cutar corona, bayan da wani dan kasar Italiya mai shekaru 44 ya shigo kasar tare da sauka a filin jirgin saman Murtala Muhammad.

A ranar 27 ga watan Fabrairu ne mutumin wanda yake aiki a wani kamfani a jihar Ogun ya fara fuskantar alamomin cutar corona wanda kuma daga baya aka tabbatar da yana dauke da cutar.

Wannan dai ya biyo bayan gwajin da aka aika da samfurinsa jihar Lagos karkashin cibiyar dakile yaduwar cututtuka ta kasa NCDC wanda kuma ministan lafiya Dakta Osagie Ehanie ya tabbatar da bullar cutar a Najeriya.

Daga nan ne cutar ta ci gaba da bazuwa sakamkon shigowar baki, abinda ya tilastawa hukumomi daukan matakan da suka dace na takaita yaduwar cutar, ciki har da sanya dokar kulle da kuma samar da kwamitin kar ta kwana mai yaki da cutar karkashin gwamnatin tarayya.

Sai dai tun a lokacin kwararru sun yi zargin cewa rashin gaggauta rufe iyakokin kasar nan da kuma rashin samar da wadatattun cibiyoyin gwaji har ma da rashin yin gwajin ga al’umma na cikin dalilan da ya ta’azzara yaduwar cutar.

Baya ga nan kwarrun sun ce, akwai rashin daukan matakin gaggawa daga wasu gwamnonin jihohin kasar nan na rashin aiwatar da dokar kulle da kuma karya ka’idojin dokar ta kulle da sauran dokoki.

Sai dai tun bayan bullar cutar Najeriya ta fuskanci nau’ikan cutar guda hudu da suka rika yaduwa kamar wutar daji, wanda daga baya kuma aka fara samun raguwar masu kamuwa da cutar a cikin shekaru biyun da suka gabata.

Tun daga wancan lokaci zuwa ranar juma’ar da ta gabata dai kididdiga ta nuna cewa yan Najeriya sama da dubu dari biyu da hamsin da hudu da dari hudu da sittin da shida ne suka kamu da cutar, cikin su kuwa guda dubu dari biyu da arba’in da takwas da dari takwas da sittin da uku sun warke bayan sun samu kulawa, sai kuma guda dubu uku da dari daya da arba’in da biyu da suka rasa rayukan su sanadiyyar cutar a jihohi 36 da birnin tarayya Abuja.

Najeriya ta fara rarraba rigakafin cutar corona samfurin AstraZeneca a watan Afrilun 2021 daga baya kuma aka ci gaba da rigakafin ta moderna, da kuma Pfizer Bio-N-Tech.

Sai dai duk da haka ana zargin karancin rigakafin ya haddasa rashin isa ga yawan al’ummar da kasar ke da shi, duk da cewa gwamnatin tarayya ta sanya dokar tilastawa ma’aikatanta yin rigakafin.

Hakan ne yasa gwamnatin tarayya a ranar 18 ga watan Fabrairun da muke ciki ta raba rigakafin cutar corona falle daya samfurin Johnson & Johnson domin ta wadatar ga dukkanin al’umma da yawanta ya kai miliyan 20 wanda ake tsammanin zai iya isar sama da kaso 18 cikin dari na yawan yan Najeriya da suka cancanci karbar allurar.

Cikin matakan da aka sanya na takaita yaduwar cutar akwai bada tazara tsakanin mutane da kuma sanya takunkumi da kuma yawan wanke hannu da sinadarin kashe kwayoyin cuta da sauran su.

Sai dai ko yaya tasirin cutar corona yake har yanzu a Najeriya? Ku biyo mu domin jin martanin masana.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!