Connect with us

Labarai

NiMet ta yi hasashen samun ruwan sama hade da tsawa a wasu jihohin arewacin kasar nan

Published

on

Hukumar kula da yanayi ta kasa NiMet ta yi hasashen cewa za a samu ruwan sama mai hade da tsawa a wasu jihohin arewacin kasar nan tun daga yau Asabar zuwa ranar Litinin, tare da yiwuwar iska mai karfi a wasu yankuna.

 

Hukumar ta bayyana hakan ne cikin wata sanarwar da ta fitar, inda ta ce ana sa ran ruwan saman zai shafi jihohi da dama da suka hadar da Taraba, Adamawa, Kaduna, Borno, Bauchi, Gombe, Jigawa, Katsina, Kano, Zamfara, Sokoto, Kebbi da Yobe a lokuta daban-daban cikin kwanaki ukun.

 

NiMet ta yi gargadin cewa tsawa da iska mai ƙarfi na iya haddasa haɗari, don haka ta shawarci jama’a da su guji shiga ko tuka mota cikin yanayin na ruwan sama, kana su guji fakewa ƙarƙashin manyan bishiyoyi.

 

Hukumar ta kuma bukaci kamfanonin jiragen sama da sauran masu ruwa da tsaki su rika bibiyar rahotannin yanayi kafin gudanar da ayyukansu domin kare rayuka da dukiyoyin al’umma.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!