Kiwon Lafiya
Nan da lokaci kaɗan za a samu karuwar masu lalurar kurumta – Dr. Ado Soron Ɗinki
Wani kwararren likitan Kunne Hanci da Makogaro a asibitin Muhammad Abdullahi Wase a nan Kano ya ce, faruwar lalura a makogaro kan haifar da cuta ga kunne a dalilin alakarsu tun a halitta.
Dr. Ado Hamza Soronɗinki ne ya bayyana hakan jim kadan bayan kammala shirin Barka da Hantsi na Freedom Radio.
Dr. Ado Hamza Soronɗinki ya ce, ana samun matsala a kunne sakamakon wasu ayyukan da dan adam ya ke yi a kankin kansa, da suka hadar da sanya duk wani nau’in abu domin sosa kunnen, ko kuma shan ruwa mai sanyi.
“Baya ga wannan ma akwai sanya na’urar sauti a kunne ba tare da saisaita sautin da ya kamata kunne ya saurara ba,sannan wankan kududdufi na haddasa ciwon kunne saboda cututtukan dake cikin ruwan
Kazalika likitan ya kuma ce, shayar da jarirai a kwance da kuma rashin duba su yadda ya kamata bayan an haife su na haifar musu da matsala a kunne.
Ko da yake bayani kan karuwa ko raguwar masu fama da matsalar kunne a yanzu, Dr. Ado Hamza Soronɗinki cewa yayi, “A nan Kano ba a samu sauyi mai yawa ba saboda yanzu mutane sun fara gane abubawan da suke yi dake janyo musu ciwon kunnen”.
Likitan ya kuma ce, matukar matasa za su ci gaba da sanya irin wadannan nau’rori ba tare da neman shawarar likita ba, to kuwa za a samu karuwar masu lalarar kurumta nan ba da jimawa ba.
A ranar 1 ga watan Maris ne ake gudanar da bikin ranar ji ta duniya wanda majalisar dinkin duniya ta ware da nufin fito da matsalolin da kunne ke fuskanta da kuma lalubo hanyoyin magancewa, tare da wayar da kan al’umma kan yadda ya kamata su kula da lafiyar kunnen su.
You must be logged in to post a comment Login