Coronavirus
Nasir El-Rufa’i ya warke daga cutar Corona
Gwamnan jihar Kaduna Malam Nasir EL Rufai ya warke daga cutar Corona
Malam Nasir El Rufai ya bayyana cutar ta Corona a matsayin barazana ga al’umma inda yace ba zai so koda makiyin sa ya kamu da cutar ba.
Gwamna EL Rufai ya bayyana haka a wani jawabi da yayi kai tsaye ga al’ummar jihar ta Kaduna.
An gwada Malam Nasir EL Rufai ne a ranar 28 ga watan Maris, bayan bayyana cewa yana dauke da cutar ta COVId 19 Gwamnan ya killace kansa daga nan ne kuma kwararru a fannin lafiya suka fara duba shi.
Yace masu duba shi sun fito ne daga asibitin Barau Dikko da kuma jami’an maaikatar lafiya ta jihar Kaduna.
Gwamna EL Rufai yace ya godewa Allah madaukakin sarki sakamakon warkewa da yayi da kuma tausaya masa da al’umma suke yi da adduoi tun lokacin da ya bayyana cewa ya kamu da cutar ta COVID 19.
Yace bayan damuwa da iyalansa suka yi na iya rasa shi sun kuma shiga dimuwa na tunanin suma ka iya kamuwa da cutar ta COVID 19.
Yace iyalan nasa sun taimake shi da tallafa masa sannan kuma abokan aikinsa gwamnoni da kuma abokai daga kowanne sashi na Duniya sun aiko masa fatan alheri da adduoi na waraka.
Covid-19: An kori limamin jumu’a a Kaduna
Nasir El Rufa’i ya dakatar da zuwa Masallaci da Majami’U
Gwamna Nasir Ahmad EL RUFAI ya godewa kwamitin kar ta kwana na yaki da cutar CORONa ta jihar wanda Dr Hadiza Balarabe ke jagoranta tare da jamian tsaro domin kokari da suka yi na dakile yaduwar Cutar ta CORONA a jihar ta Kaduna.
Gwamna EL RUFAI bai tsaya anan ba yace yaji dadin warkewa da yayi tare da adduoi da goyon bayan al’ummar jihar Kaduna zai ci gaba da kokartawa ya ga cewa ko kadan daga al’ummar jihar ta Kaduna basu kamu da cutar ta COVID 19 ba.
Yace a yanzu babban abunda suka dame shi shine fito da tsare tsare na yin rigakafin cutar ta COVID 19 sakamakon rashin isassun kayan kula da lafiya
Malam Nasir Ahmad EL RUfai ya kara da cewa yaji dadi sosai sakamakon sallamar mutane hudu da aka yi da kuma na biyar din amma duk da haka an samu wasu Karin mutum uku da suka kamu da cutar ta COVID 19.
Yace mutum uku za’a kula da su sosai da basu kulawar da ta kamata inda yace dole ayi aiki tukuru domin kawar da cutar ta Covid 19 daga jihar ta Kaduna.
Gwamna Nasir Ahmad EL Rufai ya kara da cewa jihar Kaduna na kasa kasa a cikin jihohin da al’ummarta suka kamu da cutar ta COVID 19 sakamakon tsaurara matakai da gwamnati tayi.
Gwamnan na jihar Kaduna yace mai cutar zai iya yin sati biyu ba tare da yaji alamun ta ba kuma ba tare da ya sani ba yana iya yada ta ga na kusa da shi saboda haka ne yace cakuduwa da mutane ba dai dai bane.
Yace kadan na alamun cutar shine wasu kan fuskanci ciwon kai da tari kuma daga baya su warke amma mutane masu yawan shekaru da masu hawan jinni da cutar sukari na cikin babbar matsala ta yanke kauna daga b cutar.
Sannan Gwamna Nasir Ahmad EL RUFAI yace ya yi wa dokar kare kai daga cutar ta COVID 19 kwaskwarima inda yace duk wani dan jihar Kaduna da zai fita sai sai ya saka takunkumi a fuskar sa.
Ya kara da cewa gwamnatin jihar Kaduna zata samar da abubawan kare fuskar kyauta ga marasa karfi wanda kuma yake da karfi ya dinka wanda hakan ne zai kare kansa da na kusa da shi daga cutar.
Sannan yayi kira ga al’umma da su zauna a gida tare da bayar da tazara da kuma daina haduwa da mutane da suka wuce mutum 10 tare da wanke hannu da ruwa da sabulu akai akai.
You must be logged in to post a comment Login