Connect with us

Labarai

Shugaba Tinubu ya ta ya al’ummar Hausawa murnar ranar Hausa

Published

on

Shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu,  ya taya al’ummar Hausawa murna ta ranar Hausa, da ya ce manyan ginshiƙai ne da ke taka muhimmiyar rawa wajen tabbatar da haɗin kan kasar nan  da ci gabanta.

 

Tinubu  ya ce Babu shakka, harshen Hausa ya bunƙasa, ya kuma zama ɗaya daga cikin manyan harsunan haɗin kai da kasuwanci a sassa daban-daban na duniya.

 

A cikin saƙon da ya wallafa a shafinsa na X, shugaban ya ce Hausawa na taka muhimmiyar rawa wajen haɗin kai da ci gaban Najeriya 

 

Shugaban ya taya  al’ummar Hausawa murna bisa bikin Ranar Hausa, wanda ake gudanarwa a yau a fadar tarihi ta Daura, dake jihar Katsina.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!