Labarai
Nazari kan kungiyoyin tsaro na al’umma
Kamar yadda aka sani al’umma na kafa kungiyoyi a yankunan da suke don taimakawa marasa galihu a cikin unguwanni tare da tallafawa jami’an tsaro wajen gudanar da ayyukan su.
Irin wadannan kungiyoyi sun taka rawar gani wajen magance matsalolin shaye-shaye da rikicin daba, wanda a baya ya addabi wasu unguwannin dake cikin birnin Kano.
Haka zalika irin wadannan kungiyoyi na ci gaban al’umma kan gaza samun tallafi daga gwamnati da mawadata dake irin wadannan unguwanni duk kuwa da irin kokarin da suke na tabbatar da ci gaban yankunan nasu, duk kuwa da irin baraza da suke fuskanta musamman a lokacin gudanar da ayyukan samar da tsaro.
Sai da wasu na ganin cewa irin wadannan kungiyoyi suna wuce gona da iri a yayin gudanar da ayyukan su.
Ana zargin cewa wasu daga cikin irin wadannan kungiyoyin na daukar doka a hannu a duk lokacin da suka kama wani mai laifi.
Wasu mutane da muka zanta da su sun bayyana ra’ayoyinsu su kan yadda kungiyoyin ke gudanar da ayyukan su.
Malam Usman Aliyu, shine shugaban kungiyar tsaro dake unguwar Dorayi Tinga, yayi karin bayani kan iron yadda suke gudanar da ayyukan nasu.
LABARAI MASU ALAKA
Akwai bukatar karin kungiyoyin tsaro a Kano
Anyi kira ga shugaba Buhari da ya kawo karshen matsalar tsaro
Kaduna za ta karbi tsarin tsaro na AMOTEKUN
Shima shugaban kwamitin samar da tsaro na unguwar Dabino dake Tukuntawa Malam Auwal Soja, ya bayyana cewa iyaye na taka rawar gani wajen boye ‘ya’yan su da suke aikata laifuka tare da dakile ayyukan kungiyoyin.
A nasa bangaren mai magana da yawun rundunar ‘yan sanda ta jihar Kano DSP Abdullahi Haruna Kiyawa, cewa ya yi rundunar su na bada hadin kai wajen kafa irin wadan nan kungiyoyi a unguwanni don tabbatar da tsaro a kowane yanki.
Ya kuma ce ba gaskiya bane zargin da ake yi wa hukumar na sakin masu laifi da irin wadan nan kungiyoyi suke kamawa.
DSP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya kuma shawarci al’umma dasu rinka bawa irin wadan nan kungiyoyi hadin kai a koda yaushe tare da kira ga kungiyoyin da su kaucewa daukar doka a hannu.
Daga
Aminu Abdullahi Ibrahim
You must be logged in to post a comment Login