Labarai
NCDC:An samu karin mutane 37 da suka kamu da zazzabin lassa
Cibiyar dakile yaduwar cututtuka ta kasa (NCDC) ta ce an samu karin mutane Talatin da bakwai wadanda suka kamu da cutar zazzabin Lassa daga ranar hudu ga wannan wata zuwa goma ga wata.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun shugaban cibiyar Chikwe Ihekweazu.
Sanarwar ta ce cikin mutane dari tara da arba’in da bakwai da aka yi musu gwajin kwayar cutar daga ranar daya ga watan Janairu zuwa goma ga watan Fabrairu guda dari uku da ashirin da hudu an tabbatar da sun kamu da cutar, yayin da uku ake ci gaba da gudanar da bincike kansu, sai kuma dari shida da ashirin wadanda aka tabbatar basu kamu da cutar ba.
A cewar sanarwar dai mutanen sun fito ne daga jihohi ashirin da kuma birnin tarayya Abuja.
Ta cikin sanarwar dai Chikwe Ihekweazu ya kuma ce jihohin da aka yi gwajin cutar ga al’ummar su, sun hada da: Edo da Ondo da Bauchi da Nassarawa da Ebonyi da Filato da Taraba da Adamawa da Gombe da Kuma Kaduna.
Sauran sune: Kwara da Benue da Rivers da Kogi da Enugu da Imo da Delta da Oyo da kuma Kebbi, sai kuma birnin tarayya Abuja.