ilimi
NECO ta fitar da sakamakon jarrabawar 2021
Hukumar shirya jarrabawar kammala sakandire ta ƙasa NECO ta sanar da cewa ta fitar da sakamakon jarrabawar ɗaliban shekarar 2021.
Shugaban hukumar Farfesa Dantali Wushishi ne ya bayyana hakan lokacin da yake zantawa da manema labarai a Minnan jihar Neja.
Farfesa Dantali Wushishi ya ce, cikin ɗalibai miliyan ɗaya da dubu ɗari biyu da talatin da uku da suka yi rijistar rubuta jarrabawar a bana, ɗalibai miliyan ɗaya da dubu ashirin da shida da ɗari shida da talatin da ɗaya ne kaɗai suka rubuta jarrabawar.
A cewar sa, ɗalibai dubu ɗari tara da da arba’in da biyar, da ɗari takwas da hamsin da uku ne kawai suka samu Credit 5 ciki har da lissafi da turanci, yayin da ɗalibai dubu ɗari da casa’in da huɗu, da dari biyu da casa’in da ɗaya ne ba su samu lissafi da turanci ba.
Farfesa Dantali Wushishi ya ce, wannan ya nuna cewa, kaso sama da saba’in da ɗaya ne suka samu nasara cikin ɗari, kuma ya nuna cewa a bara an fi samun nasara da kaso sama da 73 cikin ɗari.
You must be logged in to post a comment Login