Labarai
‘Yan sanda a Jigawa sun kama mutane 17 da zargin aikata laifuka

Rundunar ’yan sandan jihar Jigawa ta ce ta kama mutane goma sha bakwai da ake zargi da aikata laifuka daban-daban a sassan jihar.
Laifukan sun hada da sata, fasa shaguna, satar shanu, lalata kayayyakin jama’a da fashi da makami.
Mai magana yawun rundunar ‘yan sandan jihar, SP Shiisu Lawan Adam, ya ce an gudanar da samamen ne a wasu kananan hukumomi bayan samun bayanan sirri.
Ya ce jami’an sun kama wasu mutane uku da ake zargi da satar babur ɗin Boxer mai darajar kusan Naira miliyan 1.2.
Rundunar ta ce an gurfanar da wadanda aka kama a gaban kotu, yayin da ake ci gaba da bincike.
Kwamishinan ’yan sandan jihar, CP Tijjani Murtala, ya ce rundunar za ta ci gaba da amfani da bayanan sirri da haɗin gwiwar jama’a wajen yaki da miyagun laifuka.
You must be logged in to post a comment Login