Labarai
Jam’iyyar NDC ta yi Allah-wadai da kalaman Jafar Jafar

Jam’iyyar NDC reshen Jihar Kano ta yi Allah-wadai da kalaman da Jafar Jafar ya yi kan Shugaban Jam’iyyar NDC na Jihar Kano, Hon. Husaini Isah Mai Riga, inda ta bayyana kalaman a matsayin, rashin girmamawa, da kuma abin da bai dace da ƙa’idar aikin jarida ba.
Jam’iyyar ta ce tana sa ran duk wani ɗan jarida zai gudanar da aikinsa cikin gaskiya, adalci, da mutunta martabar mutane, ba tare da amfani da kalamai masu tayar da hankali ko waɗanda za su iya haddasa rashin jituwa a cikin al’umma ba.
Saboda haka, Jam’iyyar NDC ta yi kira ga Jafar Jafar da ya ci gaba da gudanar da aikinsa na jarida cikin ƙwarewa da ɗa’a, tare da guje wa kalamai ko rubuce-rubucen da za su iya haifar da hargitsi ko tayar da fitina.
You must be logged in to post a comment Login