Labaran Wasanni
NFF ta nada sababbin masu horaswa
Hukumar kwallon kafa ta Najeriya NFF, ta nada wadan da za su ja ragamar shugabancin kungiyoyin kwallon kafar Najeriya na ‘yan kasa da shekaru 17 da 20 bangaren Maza da Mata.
Hakan na kunshe ta cikin wata sanarwa da hukumar ta NFF ta fitar mai dauke da sa hannun jami’in hurda da jama’a na hukumar, Ademola Olajire.
Sanarwar ta ce an nada Christopher Danjuma da Isah Ladan Bosso da Bankole Olowookere a matsayin wadan da za su jagoranci kungiyoyin.
Ta kuma kara da cewa Isah Ladan Bosso da Christopher Danjuma za su jagoranci kungiyar kwallon kafa ta Mata ta Najeriya ‘yan kasa da shekaru 20, yayin da Bankole Olowookere ya kasance mai horar da kungiyar mata ta ‘yan kasa da shekaru 17, Flamingos.
Sanarwar ta kuma ce tsohon dan wasan baya na kungiyar kwallon kafa ta Super Eagles Oladuni Oyekale zai kasance mataimaki na 1 ga Bosso a kungiyar kwallon kafar mata ta ‘yan kasa da shekaru 20 da Jolomi Atune Alli da zai zama mataimaki na 2.
Fatai Amoo, zai jagoranci kungiyar kwallon kafa ta Najeriya ‘yan kasa da shekaru 17 ta Maza ya yin da Ahmed Lawal Dankoli, ya kasance mataimaki na 1 inda Nnamdi Onuigbo ya kasance mataimaki na 2.
You must be logged in to post a comment Login