Labarai
Nijeriya ta damu kan matakin da Nijar da Mali da Burkinafaso suka ɗauka
Gwamnatin tarayyar Nijeriya, ta bayyana damuwarta dangane da matakin fita da kasashen Nijar da Mali da kuma Burkinafaso suka yi daga Ƙungiyar Ecowas.
Hakan na ƙunshe ne ta cikin wata sanarwa d mai magana da yawun ma’aikatar kula da harkokin wajen Francisca Omayuli, ta fitar da yammacin jiya Talatar makon nan.
Sanarwar ta ce, yanzu haka Nijeriya na tuntubar dukkan kasashen da ke cikin kungiyar Ecowas, domin warware matsalolin da ake fuskanta a kasashen da aka yi juyin mulki.
Haka kuma, sanarwar ta kara da cewa kofa a bude ta ke ga kasashen na Burkina Faso da Mali da Nijar ta yadda daukacin al’ummar yankin za su ci gaba da cin moriyar tattalin arziki da kimar dimukuradiyya da kungiyar ECOWAS ta amince da su.
Sanarwar ta kuma bukaci kasashen duniya da su ci gaba da bayar da goyon baya ga kungiyar ECOWAS domin samun hadin kai dangane da tsare-tsaren ƙungiyar.
You must be logged in to post a comment Login