Labarai
Nijeriya ta yi watsi da rahoton EU
Gwamnatin tarayya ta yi watsi da rahoton ƙungiyar Tarayyar Turai EU game da sakamakon babban zaɓen bana, da ya bai wa Bola Ahmed Tinubu nasarar zama shugaban ƙasa.
Cikin rahoton nata, ƙungiyar ta ce, sunan hukumar zaɓen Nijeriya INEC ya baci, musamman saboda gazawa wajen ɗora sakamakon zaben shugaban ƙasa a shafin Intanet, a lokacin da ta yi alƙawari tun da farko.
Wata sanarwa daga fadar shugaban ƙasa ta bayyana rahoton a matsayin “maras kan-gado, da aka haɗa shi ta hanyar dogaro da abubuwan da suka faru a rumfunan zaɓe ƙasa da Dubu 1 cikin Dubu 176, da aka kaɗa ƙuri’a” a ranar zaɓen na watan Fabrairu.
Sai dai har yanzu jam’iyyun adawa na PDP da Labour na ci gaba da ƙalubalantar sakamakonsa a gaban kotu.
You must be logged in to post a comment Login