Connect with us

Labarai

Nicolas Maduro ya goyi bayan tattaunawa da sulhu tsakanin yan Venezuela

Published

on

Tsohon shugaban ƙasar Venezuela, Nicolas Maduro, wanda ke tsare a wani gidan yari a birnin New York na Amurka, ya bayyana goyon bayansa ga duk wata hanya da za ta kai ga tattaunawa da sulhu tsakanin ‘yan ƙasar.

 

Ya ce tattaunawar za ta taimaka wajen tabbatar da zaman lafiya, haɗin kai da kuma sulhu a Venezuela.

 

Maduro da matarsa Cilia Flores suna tsare tun bayan da dakarun Amurka suka kama su a watan Janairu, inda ake tuhumarsu da laifukan safarar miyagun ƙwayoyi da makamai. Sai dai dukansu sun musanta zarge-zargen. Kalamansa na zuwa ne yayin da gwamnatin rikon ƙwarya da wasu jagororin adawa ke shirin fara tattaunawar siyasa a Caracas domin duba makomar ƙasar.

 

A cewar shugaban Majalisar Dokokin Venezuela, Jorge Rodriguez, tattaunawar za ta mayar da hankali kan taimakon waɗanda girgizar ƙasa ta shafa, ƙarfafa dimokuraɗiyya da kuma kare haƙƙin siyasa. Sai dai fitacciyar jagorar adawa, Maria Corina Machado, ba za ta halarci tattaunawar ba, duk da cewa ta ce ba za ta hana gudanar da ita ba.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!