Labaran Wasanni
Norwich City ta sallami Daniel Farke bayan samun nasarar wasa a Firimiya

Kungiyar kwallon kafa ta Norwich City dake kasar Ingila ta sallami mai horar da ‘yan wasan ta Daniel Farke.
Norwich dai ta sallami mai horarwar ne a ranar Asabar 6 ga watan Nuwambar 2021.
Sallamar nasa na zuwa ne awanni kadan bayan samun nasara da ya yi akan Brentford a gasar Firimiyar kasar ta Ingila da ci 2-1.
Kuma itace nasara ta farko daya samu a gasar ta shekarar 2021/2022.
Yanzu haka dai Norwich itace ta 20 kuma ta karshe a gasar Firimiyar ta Ingila da maki 5 cikin wasanni 10 da mai horarwar ya jagoranci kungiyar a bana.
Daniel Farke, dan asalin kasar Jamus, ya fara jagorantar horar da ‘yan wasan kungiyar ta Norwich City a shekarar 2017, inda ya jagoranci wasanni 208 ya kuma samu nasara a wasanni 87.
You must be logged in to post a comment Login