Labarai
INEC ta sanya ranar 9 ga Satumba domin zaɓen cike gurbi a Dawakin Kudu

Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa, INEC, ta sanya ranar Asabar, 19 ga Satumba, 2026 domin gudanar da zaɓen cike gurbi a mazabar Dawakin Kudu ta Jihar Kano.
Hukumar ta bayyana cewa za a kuma gudanar da irin zaɓen a mazabun Gombe/Kwami/Funakaye na Jihar Gombe da Sakwa da Disina a Bauchi da kuma Udu a Delta.
A cewar INEC, za a fara kaɗa ƙuri’a daga ƙarfe 8:30 na safe zuwa 2:30 na rana a rumfunan zaɓen da aka ware.
Zaɓukan na da nufin cike guraben da suka samu sakamakon rasuwa, murabus ko wasu dalilan da suka sa kujerun ’yan majalisar suka zama babu wakilai.
You must be logged in to post a comment Login