Ƙetare
Oscar Pistorius ya yi rashin nasara a bukatar sakinsa daga gidan Yari
Kotun gidan Yari a Afrika ta kudu ta yi watsi da bukatar tsohon zakaran tseren nakasassu Oscar Pistorius da ya nemi a sake shi gabanin ƙarewar wa’adinsa, shekaru 10 bayan kisan budurwarsa Reeva Steenkamp.
Yayin shari’ar a ranar Juma’a 31 ga watan Maris din bana, lauyoyin gwamnati sun bayyana cewa Pistorius bai kammala mafi karancin wa’adin da ya kamata ya shafe a gidan yarin gabanin neman alfarmar sakin na shi ba.
Lauyar da ke kare Pistorius, Tania Koen ta shaida wa Kamfanin dillancin Labaran Faransa cewa, kotun ta yi watsi da buƙatar, amma za su sake shigar da wata bukatar ta sakin sa ba badi kamar yadda doka ta tanada.
Tun a shekarar 2013 ne Pistorius mai shekaru 36 ya kashe budurwar tasa Steenkamp da sanyin safiyar ranar masoya wato Valentine ta hanyar dirka mata harsashi har sau 4 yana daga banɗaki a gidansa da ke birnin Pretoria.
You must be logged in to post a comment Login