Ƙetare
Duniya ba za ta yafe wa shugabanni ba kan yunwar da ta addabi al’umma- OXFAM
Kungiyar samar da abinci ta duniya Oxfam ta sake jaddada rahoton hukumar samar da abinci ta majalisar dinkin duniya FAO da ke cewa, akalla mutane miliyan 600 ne suke fama da matsananciyar yunwa, yayin da tace wasu karin miliyan 783 zasu iya fadawa halin yunwar nan da 2030 matukar ba’a dauki matakan kare afkuwar hakan ba.
Ta cikin wata makala da kungiyar ta Oxfam ta fitar, ta ce duniya ba zata yafewa gwamnatoci ba, matukar suka ci gaba da zura idanuwa biliyoyin mutane na mutuwa saboda yunwa, yayin da su kuma suke rayuwa irin ta alfahari.
A cewar kungiyar bayan gwamnatoci, akwai bukatar masu hannu da shuni su taka muhimmiyar rawa wajen wadata jama’a da abinci, musamman idan aka yi la’akari da irin kazamar ribar da suka rika samu a kasuwancin su lokacin annobar Corona.
Oxfam din tace babu ko tantama a rahoton hukumar abinci ta majalisar dinkin duniyar, idan aka yi duba da irin illar da sauyin yanayi ke zuwa da shi na gurbata kasar noma, da kuma tashe-tsahen hankula da suke raba jama’a da muhallan su ko kuma ma hana manoma zuwa gona.
Bayan zallar yunwar da jama’a musamman a kasashe masu tasowa zasu fuskanta, kananan yara a wasu kasashe na kokawa da rashin abinci mai
Rahoton: Ahmad Kabo Idris
You must be logged in to post a comment Login