Labarai
Tsohon shugaban hukumar kwallon kafa ta kasa Ibrahim Galadima ya rasu

Allah yayiwa tsohon shugaban hukumar kwallon kafa ta kasa Ibrahim Galadima rasuwa, a jiya Asabar bayan fama da gajeriyar rashin lafiya.
An haifi Marigayin, a ranar 15 ga Fabrairu, 1948, ya kuma jagoranci hukumar kwallon kafa ta kasa NFF tsakanin 2002 zuwa 2006, tare da ba da gudummawa wajen bunkasa harkar kwallon kafa a cikin gida da kasashen waje.
Haka kuma ya taba zama shugaban hukumar wasanni ta jihar Kano, inda ya taka muhimmiyar rawa wajen habaka wasanni tun daga matakin kasa har zuwa na kasa da kasa.
Za a gudanar da sallar jana’izarsa, a yau Lahadi, 19 ga Afrilu, 2026, da karfe 10:00 na safe a Masallacin waje dake karamar hukumar Fagge a jihar Kano.
You must be logged in to post a comment Login