Labarai
Trump ya yaba wa shugaba Tinubu bisa yaƙi da ta’addanci

Shugaban Ƙasar Amurka, Donald Trump, ya yaba wa shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu bisa matakan da ya ke ɗauka na yaƙi da ta’addanci da magance matsalolin tsaro da suka addabi Najeriya, musamman hare-haren da ke shafar Mutane da dama.
A cikin wata wasiƙa da ya aike wa Shugaba Tinubu mai ɗauke da kwanan watan 6 ga Yulin 2026, Trump ya bayyana cewa yana mutunta irin jagorancin da Shugaban Najeriya ke yi wajen tinkarar matsalolin da ƙasar ke fuskanta.
Ya kuma ce abin alfahari ne a gare shi ya tsaya tare da Najeriya a yaƙin da take yi da ‘yan ta’adda domin ganin ƙasar ta samu zaman lafiya da ci gaba.
Trump ya ƙara da cewa dangantakar da ke tsakanin Amurka da Najeriya ta ƙara ƙarfafa musamman a fannin tsaro, inda ƙasashen biyu ke ci gaba da haɗa kai wajen magance matsalolin tsaro da ke addabar wasu sassan Najeriya.
A cewar Fadar Shugaban Ƙasa, wasiƙar ta nuna irin goyon bayan da gwamnatin Amurka ke bai wa ƙoƙarin gwamnatin Tinubu na tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin al’ummar Najeriya ba tare da la’akari da bambancin addini ko yanki ba.
You must be logged in to post a comment Login