Labarai
Paul Pogba ya kamu da Corona
Dan wasan tsakiyar kungiyar kwallon kafa ta Manchester United Paul Pogba, ya kamu da cutar Coronavirus.
Mai hora da kasar Faransa, Didier Deschamps ne ya bayyana hakan, inda ya ce dan wasan mai shekara ashirin da bakwai tuni ya killace kansa na tsawon kwanaki goma sha hudu a gidan sa.
Pogba ba zai samu halartar wasan da Faransa za ta buga da kasar Sweden ba, a wasannin neman cancantar shiga gasar cin kofin nahiyar Turai ta kasa-da-kasa, da za su fafata a ranar biyar ga watan Satumba mai kamawa.
Har ila yau, akwai wasan kasar ta Faransa da za ta karbi bakwancin kasar Croatia bayan kwanaki uku da yin na kasar Sweden.
Haka kuma, kungiyar sa ta Manchester United na ikirarin cewa dan wasan ka iya taka leda a wasanta na farko da za ta hadu da Crystal Palace a gasar firimiyar kasar Ingila, wanda za a fafata a ranar goma sha tara ga wata mai kamawa.
Yayin da daukacin ‘yan wasan kungiyar ke yi masa fatan samun sauki cikin kankanin lokaci, duba da yadda sabuwar kakar wasanni ke karatowa.
You must be logged in to post a comment Login