Labarai
PDP a Gombe ta zargi gwamnati da sakaci kan kula ga ma’aikatan manyan makarantu

Jam’iyyar PDP a jihar Gombe ta zargi gwamnatin jihar da yin sakaci na nuna rashin ko in kula ga ma’aikatan manyan makarantu, bayan ƙungiyar ma’aikatan makarantun ta fara yajin aikin gargadi na kwanaki 14.
Jam’iyyar ta ce gwamnati ta yi biris da wa’adin da Ƙungiyar Haɗin Kan Ma’aikatan Manyan Makarantu na Jihar Gombe ta ba ta na kwanaki 14 domin biyan haƙƙoƙin ma’aikata da suka haɗa da ƙarin albashi da alawus-alawus.
PDP ta yi kira ga gwamnatin jihar da ta zauna da ƙungiyar, ta tsara yadda za a biya haƙƙoƙin ma’aikatan tare da hana yajin aikin tsawaita.
Ƙungiyar ta ce wasu daga cikin buƙatunta sun haɗa da mafi ƙarancin albashin naira dubu 30 na shekarar 2019, rashin aiwatar da sabon mafi ƙarancin albashin naira dubu 70 da kuma alawus-alawus.
Makarantun da yajin aikin ya shafa sun haɗa da Kwalejin Ilimi ta Billiri da Kwalejin Kimiyya da Fasaha da kuma Kwalejin Kimiyyar Lafiya da Fasaha ta Kaltungo.
You must be logged in to post a comment Login