Labarai
PDP ta yi Allah-wadai bisa tsarewar da EFCC ta yi wa Tambuwal

Jam’iyyar PDP a jihar Sokoto ta yi Allah-wadai da kamawa tare da tsare tsohon gwamnan jihar Aminu Waziri Tambuwal, lamarin da ta ce jam’iyyar APC ce ke neman jefa dimokuraɗiyyar Najeriya cikin ruɗani.
A wata sanarwa Sakataren yada labaran PDP na jihar, Hassan Sahabi Sanyinnawal ya fitar, ya ce wannan na cikin yunƙurin cin zarafi da murƙushe jam’iyyun adawa a ƙasar.
Ya ce kamen na zuwa ne a daidai lokacin da aka fara ƙoƙarin samar da haɗakar jam’iyyun adawa a ƙasar domin fuskantar zaɓe mai zuwa, inda kamen ba zai hana komai ba wajen yunƙurin da suke yi na kawo sauyi ba.
Bayan kamun nasa dai hukumar ta EFCC ta ce, ta tsare tsohon gwamnan na jihar Sokoto Aminu Waziri Tambuwal, bisa zarginsa da almundahanar kuɗi, da Rahotonni suka tabbatar da cewar sanatan ya isa ofishin hukumar ne da kansa domin amsa gayyatar da aika masa a ranar Litinin, sannan ta riƙe shi.
You must be logged in to post a comment Login