Labarai
PRP ta bukaci shugaba Tinubu ya gaggauta yin murabus kafin zaben 2027

Jami’iyyar PRP ta bukaci shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu da ya gaggauta yin murabus kafin zaben 2027.
Shugaban jam’iyyar ta PRP Dr. Hakeem Baba Ahmad ne ya bayyana hakan a zantawar sa da DCL English. In da ya ce shugaban kasa Tinubu ya gaza ta fuskar habbaka tattalin arzikin kasar nan baya ga harkokin tsaro da sauran harkokin shugabanci.
Haka kuma ya ce, manufofin gwamnatin tarayya sun haddasa tsananin rayuwa ga al’ummar Najeriya.
You must be logged in to post a comment Login