Labarai
Sojoji da taimakon dakarun CJTF sun lalata sansanonin yan ta’adda a dajin Sambisa

Dakarun rundunar sojin Najeriya tare da haɗin gwiwar ƙungiyar yan sa-kai ta CJTF sun lalata sansanonin ‘yan ta’adda a dajin Sambisa da ke ƙaramar hukumar Gwoza a jihar Borno.
Rahotanni sun ce an gudanar da farmakin ne karshen makon da ya gabata inda dakarun suka kutsa cikin wuraren da ake zargin ‘yan ta’addar ISWAP ke amfani da su a ƙauyukan Disa da Balangaje.
An ce ‘yan ta’addar sun tsere da zarar sun hango dakarun sojin, lamarin da ya bai wa jami’an damar rusa sansanoninsu da cibiyoyin adana kayan aiki da suke amfani da su.
Hukumomin soji sun bayyana cewa wannan farmaki na daga cikin matakan da ake ci gaba da ɗauka domin hana ‘yan ta’adda sake kafa sansanoni a dajin Sambisa. Sun kuma tabbatar da cewa babu wani soja da ya rasa ransa ko ya jikkata yayin aikin.
You must be logged in to post a comment Login