Labaran Wasanni
PSG na shirin raba gari da Pochettino
Kwana guda bayan lashe gasar Ligue 1 da tayi, kungiyar kwallon kafa ta PSG na shirin raba gari da mai horar da ita Mauricio Pochettino dan kasar Argentina.
PSG dai ta zama zakara a gasar Ligue 1 ta kakar wasannin shekarar 2021/2022 bayan tashi wasa 1-1 da takwararta ta Lens a ranar Asabar.
Lamarin da ya sanya shugabancin kungiyar fara daukar matakin kwaskawarima sakamakon ficewa daga gasar kofin turai a zagaye na 16 da tawagar tayi.
Tsohon mai horar da Tottenham da rahotanni a baya suka bayyana shi ne zai kasance a filin wasa na Old Trafford, sai dai kungiyar tuni ta dauki matakin amincewa da nadin Erik ten Hag a matsayin wanda zai jagoranci United a kasar wasannin shekara mai zuwa.
Wannan lamari dai ya sanya PSG daukar matakin raba gari da dan kasar Argentina wanda ake gani kungiyar na shirin sallamar ‘yan wasa da dama domin sake zubi na tunkarar kakar wasanni mai zuwa.
Sakamakon yadda tawagar ke da ‘yan wasa irinsu Lionel Messi Neymar JR da kuma Kliyn Mbappe amma ta gaza yin abin a zo a gani a gasar cin kofin zakarun turai ta kakar wasannin shekarar da muke ciki.
Wa ake sarai zai maye gurbin Pochettino?
Mai horar da kungiyar kwallon kafa ta Tottenham Antonio Conte tuni ake hasashen ka iya maye gurbinsa da zarar kungiyar ta sanar da sallamar
Pochettino.
Pochettino dai yanzu haka na jagorantar Spurs da take a mataki na shida a gasar Frimiya wanda maki biyu ne tsakaninta da Arsenal da kawo yanzu wasanni biyar ne suka rage a kammala kakar wasanni ta bana.
You must be logged in to post a comment Login