Labaran Wasanni
Qatar 2022: Gernot Rohr ya fitar da sunayen ‘yan wasa 30 a wasan Liberia da Cape Verde
Mai horas da ‘yan wasan kungiyar kwallon kafa ta Nigeria Super Eagles Gernot Rohr ya fitar da sunayan ‘yan wasan kasar 30 da za su buga wasan share fagen buga kofin Duniya na shekarar 2022 da za’a gudanar a kasar Qatar.
Za dai a buga wasannin share fagen a ranar 3 da 7 ga watan Satumba mai kamawa.
A ranar Juma’a 3 ga wata Nigeria za ta karbi bakuncin kasar Liberia, inda za’a buga wasan a filin wasa na jihar Lagos.
Sai kuma ranar 7 ga watan na satumba tawagar ta Super Eagles za ta yi tattaki zuwa kasar Cape Verde inda za ta buga wasa da kasar a filin wasan ta na Mindelo.
Daga cikin ‘yan wasan da aka fitar da sunayan nasu akwai masu tsaron raga da suka hadar da Maduka Okoye da Francis Uzoho, sai masu tsaron baya William Ekong da Abdullahi Shehu da Chidozie Awaziem da Leon Balogun.
Yayin da yan tsakiya suka hadar da Wilfred Ndidi da Oghenekaro Etebo, sai kuma ‘yan gaba Ahmed Musa da Alex Iwobi da Moses Simon da kuma Victor Osimhen.
You must be logged in to post a comment Login