Labaran Wasanni
Qatar 2022: Sancho ba zai buga wasan Andorra da Poland ba

Dan wasan gaba na Kasar Ingila da kungiyar Manchester United
Jadon Sancho, ya fice daga cikin jerin ‘yan wasan da za su wakilci Ingila a wasan neman tikitin buga gasar cin kofin Duniya da za ta yi da kasar Andorra da Poland.
Sancho dai be wakilci kasar ta Ingila ba a wasan da ta doke kasar Hungary da ci 4-0 a ranar Talata 31 ga watan Augustan shekarar 2021, sakamakon rauni da ya samu.
Yadda take wakana a hada-hadar siyan ‘yan wasa a Nahiyar Turai
Dan wasan mai shakaru 21 ba zai buga wasan da kasar tasa za ta yi ba da Andorra a gobe Lahadi 05 ga Satumbar shekarar 2021 da za’a gudanar a filin wasa na Wembley, da kuma wasan Poland a ranar Laraba 08 ga watan na Satumba.
You must be logged in to post a comment Login