Manyan Labarai
Raba masarautar Kano : Laifin ‘Yan birni ne
Daga Abdullahi Isa
Ga duk mai bibiyar irin cece-kucen da ya biyo bayan raba masarautar Kano zuwa masarautu guda hudu wanda gwamnatin jihar ta Kano ta yi, tabbas ba zai ji dadin yadda lamarin ya raba kan al’mmar jihar ba.
Ko ni da nake bako a jihar na damu matuka kan yadda na ga kawunan al’ummar jihar ya rabu sakamakon wannan batu na kirkiro sababbin masarautu a jihar Kano.
Ba ko shakka ga al’ummar kasar Rano da Gaya da Karaye da kuma Bichi, kirkiro da sababbin masarautu a yankunansu babban lamari ne da suke ganin zai taimaka musu wajen kawo ci gaba. Sai dai ga al’ummomin da ba sa wadannan yankunan, za su kalli lamarin a matsayin wani babban nakasu ga jihar Kano ta bangaren hadin kanta da mulki da bunkasa har dama izza na masarautar ta Kano ke da shi.
To amma ba a nan Gizo ke sakar ba, abin tambaya, me ya janyo wannan lamari na rarraba masarautar ta Kano? Wannan ba ko shakka batu ne mai sauki mutum ya amsa cewa, siyasa ita ce babban dalili na farko da ya janyo faruwar hakan. Wannan Kuma zamu bar shi ga su ‘yan siyasa domin bamu da cikakken hujja na dalilan da suka janyo sai dai kawai hasashe.
Wani batu da na yi nazari wanda jama’a ba su kula da shi ba, shine gudunmawa da ‘Yan birni su ka bayar wajen tabbatar da faruwar hakan. Abinda nake nufi gwari-gwari al’ummar jihar Kano mazauna birni sun ba da gudunmawa gaya wajen ganin an raba jihar Kano zuwa masarautu da dama.
Ko da ya ke anawa Fahimtar da dama daga cikin irin wadannan ‘yan birni da nake cewa sun ba da gudunmawa wajen raba masarautar Kano zuwa masarautu guda biyar, ba su ma san cewa sun aikata abubuwa da ya taka rawa wajen tabbatar da kirkiro sababbin masarautun ba. Hasalima wasu da dama a kokarinsu na neman ganin sun dakile faruwar hakan ne ma, sai su ka bige da taimakawa wajen cimma wannan buri na gwamnati.
Misali tun lokacin da batun kirkiro sababbin masarautun ya taso a watan Mayun shekarar da mu ka yi bankwana da ita (2019), ga duk mai bibiyar kafofin sada zumunta na Internet, zai ga irin cin mutunci da ke ta hakkin al’ummomin wadannan yankuna da gwamnati ta ce za ta kirkiro musu da sabbin masarautu. Hakimai wadanda daga bisani su ka zama sababbin sarakuna na wadannan kananan hukumomi na Rano da Gaya da Karaye da kuma Bichi, sun zama abin tsokana da muzantawa tsakanin ‘yan Kano mazauna birni. An rika sarrafa hotunansu kala-kala ta hanyoyi da dama wajen nuna gazawarsu wasu lokutan ma har da kima da mutuncinsu ake tabawa.
Wannan lamari dai ya yi ta wakana a kafafen sada zumunta, kuma su al’ummomin wadancan yankunan suna gani.
Dalili na biyu shine fakewa da wani bangare na siyasa da ke adawa da gwamnatin jihar Kano ya yi na nuna kamar batun masarautar don akidar su a siyasa aka yi ta. Wannan amincewa da bangaren waccan siyasa su ka yi na nuna cewa yaki da batun kirkiro sababbin masarautun lamari ne nasu, ya ba da gudunmawa wajen ganin gwamnati ta aiwatar da hakan. Wannan Kuma ya faru ne sakamakon kallon da ita gwamnati ke yi ga wadancan bangare na siyasa a matsayin wadanda ke da goyon baya a cikin birni.
[4:29 PM, 1/6/2020] Abdullahi Isa: Ya zuwa yanzu dai koma menene dalili gwamnati ta cimma burinta na kirkiro wadannan masarautu, sai dai kash! Ci gaba da kasancewar su har abada shine abin tambaya sannan rashin kasancewar su shima lamari ne abin tambaya domin kuwa koma me zai kasance nan gaba kawunan al’ummar jihar Kano zai ci gaba da rarrabuwa ne. Misali idan nan gaba aka ce wata gwamnati ta zo ta ce za ta rushe wadannan masarautu to fa za ta fuskanci fushin al’ummomin wadannan yankuna, domin yadda lamari ke nunawa za su iya bijirewa duk wani Mutum da ya yi kokarin ganin bayan wadannan masarautu nasu. Saboda haka duk wani yunkuri na rushesu nan gaba zai kara rura wutar rikici ne tsakanin ‘yan birni da mutanen wadannan yankuna.
Sannan idan aka ce wadannan masarautu sun dore sun ci gaba da kasancewa a matsayin su, mazauna birni ba za su taba ganin kimar wadannan sarakuna ba. Tabbas! In ma hakan zai faru ba a wannan lokaci ba, watakila wasu Shekarun masu yawan gaske, hakan ka iya faruwa. Haka Kuma rashin martabasu a cikin birni zai shafi walwalarsu da kara kyamar mazauna birni wanda hakan zai sa su cusawa Mutanen su kiyayya mazauna cikin birni.
An dakatar da hawan Sarki Majalisar masarautar Kano
Masarautar Kano ta mayar da wasu dagatai 5 da ta dakatar
Rikicin Gwamnatin Kano da Masarauta: Siyasa ko cigaba?
Kai koma me zai kasance nan gaba siyasa ta rigaya da ta yi illa ga jihar Kano ta bangaren al’adarta da kima da kuma martabar masarautar Kano. A Shekarun baya furta kalami na rashin da’a ga Sarkin Kano kamar Mutum ya yi ridda ne saboda kima da daraja da jama’a ke bai wa masarautar, ba wai kawai na Kano ba har ma dana wasu jihohin ke da shi ga masarautar Kano, amma abin mamaki a yanzu kafafen sada zumunta yadda ake cin mutuncin Sarkin Kano da sauran Sarakunan na jihar Kano abin damuwa ne, ya kai ya kawo a yanzu akan tituna za ka ji jama’a suna tafiya suna muzanta sarauta wanda a Shekarun baya ko a mafarki Mutum bai isa ya yi hakan ba.
Shawarata ga kanawa da Kano da Rano da Gaya da Karaye da kuma Bichi duk jihar Kano ne, ko da wasa ka da su yadda wannan al’amari na ‘yan siyasa ya yi tasirin da zai kai nan gaba ‘yan gida daya su fara gaba da juna saboda batun rarraba kan masarautu wanda zai yi matukar illa wajen kawo koma baya ga ci gaban jihar.
Sannan akwai wasu ‘yan jihar Kano da su ka yi shura wajen kara rura wutar rikicin da Kuma rarraba kan al’mmar jihar Kano ya kamata matasan jihar Kano su farga su gane cewa ba wani abu su ke ba face zagon kasa ga zaman lafiya da Kuma ci gaban jihar.
Wannan shawarace daga mai fatan alheri ga Kanawa.
Rubutu daga Abdullahi Isah