Labarai
Rabuwar kai shi ne kalubalen da muslmai ke fuskanta – Inji Limamai
Majalisar limaman masallatan juma’a ta Kano, ta ce rabuwar kawunan musulmi da ake samu shine babban kalubalen da ke kawo koma baya ga musulman kasar nan.
Shugaban majalisar ta limaman juma’a Shekh Muhammad Nasir Adam ne ya bayyana hakan yau ta cikin shirin barka da hantsi na nan tashar Freedom Radiyo da ya mai da hankali kan yadda akesamun rabuwan kawuna a tsakanin al’umma.
Muhammad Nasir Adam ya kuma ce idan har musulmin Arewa suka hade kan su yadda musulman kudancin kasar nan suka yi to babu shakka za’a samu ci gaban daya kamata a yankin na Arewa ta hanyoyi da dama.
Limamai su rika hudubar da zata kawo hadin kai Sarkin Kano
Ranar Juma’a mai zuwa za’a yi sallah babba – Sarkin musulmai
A nasa jawabin shugaban kungiyar mu Tashi mu Farka ‘yan Arewa, Malam Iliyasu Sulaiman Dorayi, kuma Na’ibin limamin masallacin juma’a na Hajji Kam, cewa yai samun hadin kan dariku na Addinai a Arewacin kasar nan zai kau da Talaucin da ake yawan samu a yankin na Arewa.
Malam Iliyasu Sulaiman Dorayi, ya kuma ce a yanzu an samu hadin kai tsakanin kungiyoyin izala da kadiriya da Tijjani a nan Kano ta yadda suke magana da murya daya.
You must be logged in to post a comment Login